Wq/ha/Lauren Bacall
Appearance
Lauren Bacall (an rada mata suna Betty Joan Perske; 16 Satumban 1924 - 12 August 2014) ta kasance jarumar fim na Amurka kuma ‘yar wasan kwaikwayo ta fage. Ta kasance mata ga Humphrey Bogart har bayan mutuwarsa, sannan daga bisani ta auri Jason Robards.
Zantuka
[edit | edit source]- Mata nawa ne wanda muka sani wanda har yanzu Clark Gable, William Powell, Cary Grant, Spencer Tracy da kuma Fredric March ke sumbantan su? Guda daya ce kawai: Myrna Loy. Sannan wacece ta sa Franklin D. Roosevelt ya ji sha’awa har ya soke Taron Yelta? Myrna Loy. Kuma duba ka ga wace mace ce a wani hoto ne John Dillinger yayi wautar fitowa daga inda yake boye ya sadu da harsashin-da ya janyo mutuwarsa a kan titin Chicago? Myrna Loy, a cikin diraman Manhattan Melodrama.
- Daukan nauyin tunawa da Myrna Loy a Zauren Taro na Carnegie kamar yadda aka hakayo acikin The New York Times (January 10, 1985).